✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari da Osinbajo za su kashe N5.24bn wajen tafiye-tafiye a 2023

Za a kashe wa Gidan Gwamnati biliyan N7.2 a kasafin da sai an ciyo bashin triliyan N10.78 domin aiwatarwa.

An ware Naira biliyan 3.34 domin tafiye-tafiyen Shugaban Kasa da Mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo a kasafin kudin Najeriya na 2023.

Haka kuma shugaban da mataimakinsa za su kashe Naira miliyan 179.28 wajen abinci, sannan za a kashe Naira billiyan 7.20 wajen kula da Gidan Gwamnati.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da daftarin Kasafin Kudin badi na Naira tiriliyan 20.51 a Majalisar Dokoki ta Tarayya.

Wannan Kasafin Kudin na badi, shi ne na takwas kuma na karshe da Muhammadu Buhari ya gabatar a matsayinsa na Shugaban Kasa, sannan shi ne Kasafin Kudi mafi yawa a tarihin Najeriya.

Kasafin Kudin ya yi hasashen samun kudaden shiga Naira triliyan 9.73, wanda hakan ke nufin akwai gibin Naira triliyan 10.78, gibin da ya kai kashi 4.78% na kasafin, wanda ya zarce kashi 3% da Dokar Kudi ta 2007 ta tanada a matsayin ka’ida.

Zuwa karshen watan Yunin bana, ana bin Najeriya a cikin gida da kasashen waje bashin Naira tiriliyan 42.8, ciki har da Naira tiriliyan 4.2 da aka ciyo bashi don cike gibi da a aka samu a kasafin bana.

Da yake jawabi a gaban majalisar, Shugaba Buhari ya ce za su ciyo bashi ne domin cike gibin Kasafin Kudin.

A cewarsa, Kasafin Kudin “Shi ne na karshe da zan gabatar wa Majalisar Dokoki ta Tarayya, kafin karewar wa’adin mulkina na karshe a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.”

Haka kuma an yi kasafin a kan canjin Naira 435.57 a kan Dalar Amurka daya, da hasashen samun gangar mai miliyan 1.69 a kullum a kan farashin Dala 70 a kowace ganga.

Yadda muka kashe kasafin 2022 –Buhari

Da yake bayani kan Kasafin Kudin bana, Shugaba Buhari ya ce zuwa 31 ga Yulin bana, Gwamnatin Tarayya ta samu kudin shiga Naira triliyan 3.66, wanda yake daidai da kashi 63 na kudin da ta yi hasashen samu, wanda bai rasa nasaba da rashin samun kasuwancin mai sosai.

A bangaren kashe kudaden kuwa, ya ce sun kashe Naira triliyan 8.29 daga cikin Naira triliyan 17.32 da suka kafasta zuwa watan Yulin na bana.

Ya ce sun kashe Naira triliyan 3.09 wajen biyan basussuka ne, sannan suka raba wa ma’aikatun gwamnati Naira triliyan 1.48.

Yadda za a kashe kasafin 2023

Da yake bayani kan Kasafin Kudin badi, Shuga Buhari ya ce daga cikin Naira tiriliyan 20.51 da za a kashe, za a yi amfani da Naira triliyan 6.557 wajen biyan basuka.

Yadda za a kashe kudin a dunkule:

  • Ayyukan Yau da Kullum:  Naira tiriliyan 8.271.
  • Biyan Basuka: Naira tiriliyan 6.557.
  • Manyan Ayyuka: Naira tiriliyan 4.934.
  • Hukumomin Gwamnati: Niliyan N722.109.

Ma’aikatu masu kaso mai tsoka

Daftarin kasafin ya kuma nuna bangaren tsaro ne ya fi samu kaso mai tsoka, inda aka ware masa Naira tiriliyan 1.091, sai Ilimi a matsayi na hudu da Naira biliyan 663.971, sai lafiya mai Naira biliyan 508.8; a yayin da Ma’akatar Noma ta zo a matsayi na 10 da Naira biliyan 85.4.

Jerin ma’aikatu da hukumomi 10 masu kaso mafi tsoka:

  1. Tsaro – Tririliyan N1.1.
  2. Albashi – Biliyan N921.1.
  3. Harkokin ’Yan Sanda – Biliyan N777.4.
  4. Ilimi – Biliyan N663.971.
  5. Lafiya – Biliyan N580.8.
  6. Harkokin Cikin Gida – Biliyan N277.7.
  7. Wasanni da Matasa – Biliyan N187.1.
  8. Mashawarci kan Tsaro – Biliyan N166.
  9. Harkokin Waje – Biliyan N93.4.
  10. Noma da Raya karkara – Biliyan N85.4.

ASUU: Buhari ya ware N470b domin inganta jami’o’i

Haka kuma shugaban ya ware Naira biliyan 470 domin samar da kayan aiki da inganta karatu a jami’o’i a kasafin na 2023.

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya Kungiyar ASUU din da ke bukatar Naira triliyan 1.2, ta yi watsi da tayin ware wa jami’o’in Naira biliyan 150 da gwamnatin ta ce za ta ware mata a rubu’i na farko a kasafin na badi.

Ya ce gwamnatinsa ba ta sanya hannu a yarjejeniyar da yake da yakinin cewa ba za su iya cikawa ba.

Ya kara da cewa gwamnati kadai ba za ta iya magance matsalolin bangaren ilimi ba, inda ya ce: “A kasashe da dama, harkar ilimi na rataya ne a hadakar tsakanin gwamnati da mutane, musamman ma karatun manyan makarantu.”

Kasafin shekara 7 da suka gabata a sikeli

Masana tattalin arziki sun bayyana cewa a kasafin kudi bakwai da Shugaba Buhari ya gabatar a baya masu gibi ne, ta yadda abin da ake shirin kashewa ya zarce kudaden shiga da gwamnati ke hasashen samu a shekara.

Abubakar Aliyu, masanin tattalin arziki kuma jami’in huldar hada-hadar hannun jari ya ce, idan aka yi kasafi mai gibi, to sai an nemo ko an ciyo bashi domin kudaden da za a cike gibin da aka samu.

Dalilin da Buhari ke yin kasafi mai gibi

Farfesa Garba Ibrahim Sheka na Jami’ar Bayero ta Kano ya ce, “Tun da Buhari ya zo, kudin da ake samu [a gwamnati] bai kai wanda ake kashewa ba saboda haka duk shekara sai ka ji za a karbo bashi saboda za a cike gibin kasafin kudi.”

Ya ce Buhari yana irin wannan kasafi ne bisa fahimtar mazhabar tattalin arziki da ke ganin ita ce hanyar bunkasa tattalin arziki.

“Idan Allah Ya sa an dora kasafin a kan bangarorin tattalin arziki da za su kawo cigaba da bunkasa masana’antu da harkar noma da sauransu, wadanda su ne idan an bunkasa su arziki zai rika zagayawa [tsakanin jama’a].

“Idan ka tabbatar za ka samu Naira 100 sai ka yi lissafin Naira 150, to idan ka samu Naira 120, to ka ga Naira 20 da ta shigo ba ta cikin lissafinka, jajircewarka da takura wa kanka ne ya sa ka samu.”

Amma ya ce, irin wannan kasafi da bashi ake cike shi, domin daga karshe kasafin da aka yi doka yake zama, don haka sai an aiwatar da shi.

“Hakan ne ya kai kasar ga halin irin bashin da ke kanta yanzu.”

‘Bashi ya durkusar da Najeriya’

Abubakar Aliyu ya ce, shi ya sa “Tun da farko mun yi mamakin ganin ana kasafi na tiriliyoyin Naira, alhali kasar ba ta iya samun wadannan kudade.

“To a hankali ana cike gibin nan da basussuka, har yanzu aka kai ga a shekara bakwan nan, basussukan da aka rika karba ana cikin gibin sun zo sun durkusar da kasar.

“Hakan ya sa a rubu’in farko na wannan shekara, an biya bashi da kudaden da muke samu a cikin gida, har ma sai da aka kara da ciyo bashi na kashi 120 cikin 100,” inji masanin tattalin arzikin.

Ya bayyana cewa a tsawon shekara bakwai da suke gabata, “abin tsoro shi ne kudaden da aka ciyo bashi domin manyan ayyyuka, zan iya cewa ba a yi ayyukan ba kuma kudaden babu su.

“Na san bashin da aka karba na Dala biliyan 5.5 a hanyar sayar da hannun jarin Euro Bond, domin gyara tashar wutar lantarki ta Mambilla da gyaran filayen jiragen sama da biyan ’yan kwangila.

“Amma daga baya Ministan Lantarki ya fito yana cewa ko share filin ba a yi ba.”

Bangaren da ya fi samun kaso

Masanan sun bayyyana cewa, bangarorin tsaro da manyan ayyyuka da abubuwan more rayuwa da noma da masana’antu su ne suka fi samun kaso mai tsoka a kasafin shekara bakwai da suka gabata.

Farfesa Sheka ya ce, Buhari ya ba da fifiko a kan bangaren noma ne saboda “ana so a ciyar da kai.

“An rufe boda saboda a irin karfin da za a iya noma shinkafa da sauran abubuwa.

“An fito da abubuwa da dama, kamar ba wa manoma wani bashi kyauta-kyauta, wanda bankin CBN ya jagoranta,” a cewar Farfesa Sheka.

A cewar Abubakar, wani bangaren da ya samu kaso mai tsoka, shi ne bangaren gudanar da gwamnati, wanda a cewarsa bai kamata ba.

“Yaya za a yi ka karbi basuka ka yi wananna abubuwan da su?”

Bangaren tsaro ya samu kaso mai tsoka ne saboda matsalolin da kasa ke fuskanta ta wannan bangare, kama daga ta’addancin Boko Haram zuwa ’yan bindiga da ’yan aware da sauransu.

Batun manyan ayyuka kamar yadda suka bayyana, ya samu kaso mai yawa ne saboda ayyukan gina titunan jirgin kasa da hanyoyi mota, “wadanda ga su nan ana ta yi.”

Shin ko kwalliya ta biya kudin sabulu?

Abubakar Aliyu ya ce kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba a kasafin shekara bakwai da suka gabata.

Yaki da talauci

Game da tsarin bayar da rance ko tallafi, ya ce: “Abin mamaki shi ne, babu wani tsari na cewa za a yi yaki da talauci.

“Yaki da talauci ba wannan hanya za a bi ba. Yaya za ku bai wa mutane kudi, ba ku tura su wurin sana’a ba? Wannan, idan ma kudaden na isa hannunsu ke nan,” inji shi.

Bangaren Noma

Farfesa Sheka ya ce akwai sauran rina a kaba a bangaren noma, domin duk da tallafi da rance da sauran matakan da gwamnati ta dauka kan ganin an ciyar da kai.

“Sai ya zama wadda ake nomawa a gidan na ta neman ko ma ta fi ta wajen tsada, ko kuma suna kan-kan-kan.

“Ka ga a iya cewa ba a ci nasara ba, domin ana noma ta a gida amma farashi bai sauka ba, sai dada hauhauwa ma yake, har ana maganar da za a bude boda a shigo da ta wajen, talakawa su samu sauki, da ya fi.”

Manyan ayyuka

Game da abubuwan more rayuwa, malamin jami’ar ya bayyana cewa hakika ana yi.

“Amma more rayuwar ba ta zo ba saboda amfanin mutun ya gina abu shi ne ya yi amfani da shi.”

Amma a cewarsa, duk da cewa Buhari ya dora a kan gina titin jirgin da Gwamnatin Jonathan ta fara kuma yana gina tituna, rashin tsaro a kan hanyoyin sufurin tamkar an yi baya babu zani ne.

Kasafin 2023

Da yake hasashen abin da kasafin 2023 zai kunsa, Abdullahi Aliyu ya ce, yana ganin ba za ta sauya zane ba, lura da abin da aka saba gani a kasafin shekara bakwai da suka gabata.

Sai dai ya ce babu mamaki, “A kara wa bangaren zartarwa kaso saboda bukatun gudanar da gwamnati da na siyasa, kamar yin zabe da sauransu.”