✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ko Obasanjo: Wa ya raba kan ’yan Najeriya?

Shugaba Obasanjo da Shugaba Buhari na zargin juna da raba kawunan 'yan Najeriya

’Yan Najeriya sun yi sabani wajen bayyana ra’ayoyinsu a kan kalaman tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo na baya-bayan nan.

Shi dai Shugaba Obasanjo ya ce ne Najeriya na daf da durkushewa sannan kawunan ’yan kasa sun rarrabu sakamakon rashin iya tattalin bambance-bambancen da ke tsakanin al’umma a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.

“Tsofaffin bambance-bambance wadanda suka fara bacewa sun kara bayyana, sannan kusan a ko’ina gangar kyamar juna da wake-waken raba-kasa da a-ware na ta tashi ba kama hannun yaro”, inji Cif Obasanjo.

Shugaba Obasanjo ya furta wadannan kalamai ne yayin wani taro da ya yi da shugabannin kungiyoyin kare muradun wasu kabilu da na shiyya-shiyya ranar Alhamis din makon jiya.

Rarrabuwar kawuna

Sai dai kuma, a martanin da ya mayar a madadin Fadar Shugaban Kasa, Mai Magana da Yawun Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ya zargi tsohon shugaban kasar da kasancewa “Babban mai raba kan al’umma”.

“A kalamansa na bayan nan, tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yi yunkurin raba kan al’umma yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ke ci gaba da yayata [bukatar] gina kasa da hadin kan Najeriya.

“Bambancin a bayyane yake: daga matsayi mai daraja na Babban Kwamandan Rundunoni na Kasa, Janar Obasanjo ya wuntsulo zuwa matsayi mai kaskanci na Babban Mai Raba Kan Al’umma”, inji Malam Garba.

Ita ma dai Kungiyar Tuntubar Juna ta Dattawan Arewa (ACF) kakkausar suka ta yi ga Shugaba Obasanjo, tana zargin shi da yarinta.

A wata hira da jaridar Daily Trust, Shugaban Kungiyar kuma tsohon Ministan Aikin Gona Audu Ogbeh, ya ce ba wanda ya aiki Obasanjo ya sa ido a kan sauran shugabannin kasa.

“Shela cewa [Najeriya ta dauki hanyar durkushewa] kuruciya ce.

“Bari na yi adalci na fada wa Obasanjo wani abu: koyaushe akwai shi da jin cewa sai yana nan komai zai yi daidai.

“Shi ma ya fuskanci nasa kalubalen – ina batun Zaki Biam da Odi?

“Abin da aka yi musu dimokuradiyya ne?

“Kai ba duba-gari ba ne da wani ya nada don ka sa ido ko ka lura da ayyukan sauran shugabannin kasa”, inji shi.

‘A girmama na gaba’

Ita kuwa babbar jam’iyyar adawa ta PDP Obasanjo ta goya wa baya.

A ganinta, Shugaba Obasanjo ya yi abin a yaba, kuma kalamansa yunkuri ne na ceto Najeriya.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Uche Secondus, a wata sanarwa mai dauke da sa-hannun kakakinsa, Ike Abonyi, ya ce kamata ya yi “Shugaba Buhari ya daina tinkaho alhali kasar na tangal-tangal a karkashin mulkinsa”.

Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Buhari da ta girmama na gaba.

Tun da farko dai jam’iyyar APC mai mulki, ta bakin Mataimakin Kakakinta na Kasa Yekini Nabena, ta yi watsi da kalaman Cif Obasanjo ne tana cewa ba shi ma da bakin yin tsokaci a kan al’amuran da suka shafi kasa har sai ya dawo da wasu kudade da aka kashe a lokacin mulkinsa.

‘Mai bunu a gindi…’

“Abin da daure kai a ce ’yan siyasar da suka aza harsashin tabarbarewar kasa suka gina ginshikin almundahana, da zaizayewar tarbiyyarmu wai su ne masu magana a kan ci gaban kasa.

“Kamata ya yi tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya fara fada mana inda wutar lantarki take duk da Dala biliyan 16 da aka kashe [a lokacin mulkinsa] tukunna”, inji Nabena.

Ko da yake ya yarda da Obasanjo a kan cewa abubuwa sun kara tabarbarewa a zamanin Shugaba Buhari, tsohon gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, ya ce a wannan lamari mutum ne ya take laifinsa yake hangen na wani.

“Obasanjo bai fadi gaskiya ba, kuma ban yi mamakin rashin gaskiyarsa ba, saboda ya taimaka wajen kazanta al’amura ga Buhari.

“Da ya yi abin da ya dace, wadanda suka gabace da wadanda suka biyo bayanshi ma sun yi abin da ya dace, da kwabar ba ta yi wa Buhari ruwa haka ba.

“Yanzu lamarin ya fi karfin Buhari”, inji shi.

‘Ba sabon abu ba ne’

Da yake fashin baki ga jaridar Daily Trust a kan batun ranar Asabar, Dokta Abubakar Kari, wani malamin jami’a kuma mai sharhi a kan al’amuran siyasa, ya ce wadannan kalamai na Obasanjo ba yanzu aka fara jin su ba.

“Ba sabon abu ba ne a yanzu a ji ko a karanta cewa Najeriya ta durkushe.

“Kalami ne mai girma matuka wanda galibi ake yin shi saboda takaicin ko bacin rai an rasa wani abu ko kuma daga bakin ’yan adawa da wadanda suke takun-saka da masu mulki”, inji shi.

Sai dai shi ma ra’ayinsa ya zo daya da na Alhaji Balarabe Musa a kan cewa duk kanwar ja ce.

“Gaskiya ne cewa kawunan ’yan Najeriya sun rarrabu ta fuskoki da dama, amma shi ma Obasanjo yana da laifi kamar wadanda yake zargi.

“Ina da matsala da yadda Obasanajo ke son nuna cewa shi mai nazari ne a kan al’amuran kasa kuma dattijo ne dan kishin kasa saboda ba ya iya boye tsanar da yake yi ga Buhari.

“A baya-bayan nan babu adalci a irin kalaman da yake furtawa a kan wannan gwamnatin – kuma kada a manta ya yi magana ne ga wani taron shugabannin kungiyoyin kabilu da na shiyyoyi wadanda suka yi kaurin suna wajen sukar Buhari”.

Idan dai ba wani abu ne ya faru ya dauki hankalin ’yan Najeriya ba, mai yiwuwa a yi kwanaki ana cece-ku-ce a kan wannan magana ta Shugaba Obasanjo.

Idan ba a manta ba, a baya Shugaba Obasanjo ya rubuta wasu wasiku ga shugabannin dake mulki a lokacin wadanda ake alakanta faduwar gwamnatocinsu da kalaman da ya yi.

Sai dai wasikar da ya rubuta gabanin zabukan 2019 ba su kai ga sauyin gwamnati ba, lamarin da ya sa wa su ke ganin tasirin kalaman tsohon shugaban kasar ya ragu, ko ma ya dusashe gaba daya.

Game da batun wanda ya raba kawunan ’yan Najeriya kuwa, ’yan kasa ne za su yi alkalanci a kai.