✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari na ganawa da Hafsoshin Tsaro

Ganawar farko bayan dawowar Buhari daga Landan.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana tattaunawa da Manyan Hafsoshin Tsaro a karon farko bayan dawowarsa ga kasar Birtaniya.

A zaman na ranar Alhamis, Shugaban Kasar zai karbi rahoto daga Ministan Tsaro, Bashir Salihi Magashi da Manyan Hafsoshin Tsaro game da yanayin tsaron Najeriya.

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro Babagana Monguno da Kuma Ministan Harkokin Waje Geoffrey Onyema da takwaransa na Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola na cikin mahalarta zaman.

Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da Shugaban Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ma sun halarci taron, wanda ke zuwa bayan dubban mayaka da kwamandojin kungiyar Boko Haram tare da iyalansu sun mika wuya ga sojojin Najeriya a Jihar Borno.

A baya-bayan nan sojojin sun jima suna ragargaza a kan maboyan kungiyar ta Boko Haram a yankin Dajin Sambisa da Dutsen Mandara da ke Jihar ta Borno da kuma maboyan ’yan bindiga a yankin Arewa Maso Yamma.

Sanarwar zaman da kakakin Shugaban Kasa, Femi Adesina ya fitar da farko ta ce Manyan Hafsoshin Tsaro za su yi wa Shugaban Kasa bayanin inda aka kwana, da kuma matsalolin da ke bukatar a lalubo musu mafita a zaman.

A sanarwar da sojoji suka fitar a baya kan mika wuyan ’yan Boko Haram din, sun ce mayakan na neman a yafe musu.

Sun danganta mika wuyan da ragargazar da sojojin suka yi musu da kuma rabuwar kai tsakanin bangarorin kungiyar da kuma rashin lafiya da yunwa da ta addabi tsoffin mayakan.

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar ta shiga cikin rudani ne tun bayan da shugabanta, Abubakar Shekau, ya yi kunar bakin wake bayan ’yan kungiyar ISWAP mai mubaya’a ga kungiyar ISIS sun ritsa shi da wasu mataimakansa domin su yi wa ISWAP mubaya’a.