✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari na son a cire sadarar da za ta hana Ministoci tsayawa takara daga dokar zabe

Shugaban ya ce sadarar ta tauye 'yancinsu na tsayawa takara.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nemi Majalisar Dattawa ta cire sadarar da ta hana masu rike da mukaman siyasa tsayawa takara daga Kundin Dokar Zabe ta 2022 wacce ya sanya wa hannu.

Shugaban ya bayyana bukatar ne a wata wasika da Shugaban Majalisar, Ahmed Lawan, ya karanta a zauren majalisar ranar Talata.

Buhari ya ce tanadin sadarar ya tauye ’yancin masu rike da mukaman siyasa na tsayawa takara kamar kowane dan Najeriya.

Hakan dai na nufin dukkan masu rike da mukaman siyasar a kowane matakin gwamnati na iya tsayawa takara ba tare da sun sauka daga mukaminsu ba.

Yayin da yake sanya hannu a kan dokar dai, Shugaban ya koka kan sashe na 84 (12), wanda ya tanadi cewa babu wani mai rike da kowane irin mukamin siyasa a kowane mataki da za a zabe shi a matsayin daliget ko wakilin jam’iyya da nufin zama dan takara.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce dai Buhari ya rattaba hannu a kan dokar, bayan shafe tsawon shekaru ana yi mata kwaskwarima.