✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya aike da sojoji Imo don tabbatar da tsaro

Buhari ya amince tare da aike da karin dakarun soji jihar.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya amince da tura karin dakarun soji da kuma makamai zuwa Imo don kawo karshen hare-haren bata-gari a jihar.

Buhari ya amince da daukar matakin ne bayan ganawa da Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma a fadarsa da ke Abuja a ranar Litinin.

“Gaba daya batun da muka tattauna ya jibanci sha’anin tsaro a Kudu maso Gabas ne da kuma yadda za a shawo kan lamarin.

“Mun tattauna kuma ya karbi shawarwarin dana baya, sannan ya bayar da umarnin aika mana karin jami’an tsaro da makamai,” cewar Gwamna Uzodinma.

Ya ce shugaban kasa ya amince da bukatarsa ta aike da karin jami’an tsaro don fatattakar tsagerun da ke kai hari kan jami’an tsaro da dukiyar gwamnati.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), ya rawaito cewa an gayyaci gwamnan ne bayan harin da aka kai gidan Shugaban Kungiyar Ohanaeze Ndi Igbo, Farfesa George Obiozor, da wasu kadarorin ’yan sanda.

Wasu tsageru sun dauki lokaci suna kaddamar da hare-hare kan jami’an ’yan sanda da kuma shugabannin al’umma a jihar.

Gwamnan ya bukaci hadin kan daukacin al’ummar jihar don tabbatar da tsaro da kuma ci gaban jihar.

Ya kara da cewa, “Muna bukatar hada kanmu, mu kasance masu gaskiya a tsakaninmu, mu himmatu wajen tabbatar da cewa gobenmu ta yi kyau.”