✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya amince a kashe biliyan 10 domin shata kan iyakoki

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince a fitar da kudi kimanin Naira biliyan 10 ga Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) domin ci gaba da shata…

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince a fitar da kudi kimanin Naira biliyan 10 ga Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) domin ci gaba da shata iyakokin kasa.

Shirin dai zai shafi kananan hukumomi 546 a fadin kasa a shirye-shiryen da ake yi na gudanar da kidayar kasa.

Mai rikon mukamin shugaban hukumar, Dakta Eyitayo Oyetunji shine ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin lokacin da yake yi wa ‘yan  jarida jawabi a kan shirye-shiryen kidayar.

Eyitayo ya kuma ce an ware karin Naira biliyan hudu da miliyan 500 a cikin kasafin kudin 2021 domin kammala shirin yadda ya kamata.

Muna tafe da karin bayani…