✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya ba ’yan kasashen waje 286 takardar shaidar zama ’yan Najeriya

86 daga cikin mutanen 'yan kasar Lebanon ne

Gwamnatin Tarayya a ranar Alhamis ta ba wasu ‘yan kasashen waje kimanin 286 cikakkiyar shaidar zama ‘yan Najeriya.

Mutanen da aka ba shaidar sun hada da ‘yan kasar Lebanon 86 da ‘yan Birtaniya 14 da wasu ’yan Amurka hudu, da sauran mutum 102 daga wasu kasashen.

Kamfanin Dillancin Labarain Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya ba wadannan mutanen takardun shaidar ne bayan sahalewar Majalisar Zartarwa ta kasa.

Kazalika rahotanni sun ce mutum 208 sun  samu takardar shaidar zama ’yan kasar ne ta hanyar haihuwa, yayin da sauran 78 kuma suka samu ta hanyar rantsuwa da karanta taken alkawuran kasa.

Da yake jawabi yayin taron shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Hukumar Kula da shige da fice ta kasa (NIS), ta basu takardar shaidar kamar yadda doka ta tanada.

Buhari ya gargade su da su zama jakadu na gari a kasar, tare da nuna kauna ga sauran al’ummar Najeriya.

A cewar shugaban, zamantowarsu ’yan Najeriya yanzu, ya sanya tarihin kasar yanzu ya zama nasu.

Tun da farko, Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola, ya ce sai da jami’an tsaro suka bi diddigin sabbin ’yan Najeriyar kafin ba su takardun Shaidar.

Ya ce Gwamnatin Tarayya ta kuduri aniyar karfafa gwiwar masu hannu da shuni, da sauran ’yan kasashen waje hanyar ba su guraben girmamawa a kasar nan.