✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya ba ’yan kasuwar da suka yi gobara a Sakkwato tallafi

NEMA na horas da jami'an Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Sakkwato

Gwamnatin Tarayya ta bayar da kayan tallafi ga ’yan kasuwar da dukiyoyinsu suka kone a gobarar Kasuwar Shagari da ke Sakkwato.

Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta ce Shugaba Buhari ya ba da tallafin kayan abinci da na ginin ne kafin a kammala bincikenn musabbabin gobarar saboda yadda gobarar ta girgiza shi.

“Kayan sun fara isa Sakkwato kuma ina ba da tabbacin cewa zuwa mako mai zuwa za a fara rarraba su,” inji Mataimakin Jami’in Kula da da tallafi na NEMA, Ajayi Oluwatope.

Ya bayyana damuwa kan girman barnar da gobaar ta yi, inda ya yi kira ga wadanda suka yi asa da su dauki abin da ya faru a matsayin ibtila’i wanda ba shi makawa.

Ya ce NEMA ta shirya wa ma’aikatan SEMA ta Jihar Sakkwato kwas kan bayar da agajin gaggawa domin inganta kwarewarsu wajen aiwatar da ayyukansu.

Darakta-Janar na NEMA, Muhammad Muhammed ya jaddada aniyar Hukumar ta inganta kwarewar ma’aikata wajen shawo kan irin wadannan matsaloli.

Mashawarci Gwamnan Jihar Sakkwato na Musamman kan Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Zubairu Albadau ya yi wa Shugaba Buhari godiya game da tallafin ga ’yan kasuwar da suka  yi asara a gobarar.