✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya ba ’yan Najeriyar da aka kwaso daga Ukraine kyautar N48,000

Gwamnatin Tarayya ta ce ta ba dukkan ’yan Najeriyar da aka kwaso daga kasar Ukraine mai fama da rikici kyautar Dalar Amurka 100, kwatankwacin Naira…

Gwamnatin Tarayya ta ce ta ba dukkan ’yan Najeriyar da aka kwaso daga kasar Ukraine mai fama da rikici kyautar Dalar Amurka 100, kwatankwacin Naira 48,000, don su rage radadi.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Abdur-Rahman Balogun, kakakin Hukumar da ke Kula da ’Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje (NiDCOM), ya fitar ranar Juma’a a Abuja.

Kamfanin Daillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa da sanyin safiyar Juma’a ne rukunin farko na ’yan Najeriya su 450 daga Ukraine din suka sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Sanarwar dai ta ce mutanen, wadanda galibinsu dalibai ne sun iso Abuja ne a wani jirgin kamfanin Max Air kirar Boeing 747, da misalin karfe 7:10 na safe.

Sai dai ya ce wadanda za a debo daga kasar Poland ba su samu tasowa ranar Alhamis ba kamar yadda aka tsara da farko, inda aka canza lokacin tashin jirginsu zuwa karfe 2:30 na ranar Juma’a.

Abdur-Rahman Balogun ya kuma ce tuni jirgin kamfanin Air Peace ya tafi kasar Hungary ranar Alhamis, kuma ana sa ran saukarsa a Abuja da misalin karfe 4:30 na yammavcin Juma’a.

Gwamnatin Tarayya dai ta ware kimanin Naira miliyan uku da rabi don kwaso ’yan Najeriyar da suka samu mafaka a kasashen makwabtan Ukraine din. (NAN)