✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya bai wa iyalan mutanen da aka kashe a Sakkwato tallafi

An raba wa iyalan kayan tallafin ne domin rage musu radadin halin da suke ciki.

Gwamnatin Tarayya ta raba wa iyalan mutanen da ’yan bindiga suka kashe a Jihar Sakkwato kayan tallafi don rage musu radadin halin da suke ciki.

Darakta-Janar na Hukumar Bada Agaji ta Kasa (NEMA) Mustapha Habib ya ce an bayar da kayan ne don rage wa iyalan radadin halin da suke ciki.

Daraktan ya samu wakilcin jami’in hukumar, Alhassan Nuhu, wanda ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bayar da umarnin kai musu tallafin.

“Shugaban kasa ne ya bayar da umarnin bayar da tallafin ga iyalan wadanda abun ya shafa don rage musu radadin halin da suke ciki,” a cewarsa.

Kayan tallafin da aka bayar sun hadar da kayan sawa, buhun shikafa 2,000, buhunan wake, gero, manja, man gyada, kwalayen sabulu wanka 100 da kwalayen sabulun wanki 100.

Ragowar kayayyakin sun hadar da tabarmi, barguna, bokitan wanka, tufafin yara da sauransu.

Da yake karbar kayan tallafin, Gwamnan Jihar Sakkawato Aminu Waziri Tambuwal, wanda ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Jihar, Sa’idu Umar, ya bayyana godiyar gwamnatin jihar a kan tallafin da aka ba wa iyalan wadanda ’yan bindigar suka kashe.