✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya bai wa Jega sabon mukami

Jega ya samu sabon mukami a zamanin gwamnatin Buhari.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada tsohon Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega a matsayin Shugaban Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Jos.

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai ranar Alhamis a Abuja, babban birnin kasar.

Sanarwar da ministan ya fitar ta ce, Shugaba Buhari ya kuma amince nade-nade gami da sauye-sauyen masu makaman Uban jami’o’in Tarayya 42 da ke fadin kasar.

Daga ciki akwai wasu tsaffin Ministoci biyu, Farfesa Anthony Anwuka, wanda aka nada Shugaban Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Albarkatun Man Fetur ta Tarayya da ke Jihar Delta da kuma Udoma Udo Udoma, a matsayin Shugaban Majalisar Gudanawa ta Jami’ar Bayero da ke Jihar Kano.

Aminiya ta ruwaito cewa, Udoma da Farfesa Anwuka sun kasance ministoci a wa’adin mulkin Shugaba Buhari na farko.

Sauran wadanda aka nada a matsayin Shugabannin Majalisar Gudanarwar sun hada da; Farfesa Ahmed Mohammed Modibbi a Jami’ar Abuja da Dokta Sonny Kuku a Jami’ar Benin.

Sai kuma Malam Adamu Fika a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Cif Ikechi Emenike a Jami’ar Najeriya wato Nsukka da kuma Ballama Manu, a Jami’ar Maiduguri.

Ministan ya ce Buhari ya kuma bayar da lamunin gudanar da sauye-sauye a Majalisar Gudanarwar Jami’o’i 23 biyo bayan karewar wa’adinsu a ranar 8 ga watan Mayun bana.

A cewarsa, za a gabatar da sabbin Uban Jami’o’in yayin bikin yaye dalibai na gaba da za a gudanar, inda kuma a nan ne za a bai wa wasu shaidar digiri ta karamci.

Daga cikin sabbin Uban Jami’o’in akwai Tor na Kabilar Tibi, Mai Martaba Farfesa James Otese Iorzua Ayatse (Jami’ar Benin), Ewi na Ado-Ekiti Oba Rufus Adeyomo Adejugbe Aladesanmi III (Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi) da Obi na Onitsha, Obi Ofala Nnaemeka Alfred Achebe (Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya).