✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya bukaci a kawo rahoton hatsarin jirgi a Legas

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce yana jiran sakamakon binciken hatsarin jirgin da ya rikoto ya fadi a rukunin wasu gidaje a Jihar Legas. A sakon…

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce yana jiran sakamakon binciken hatsarin jirgin da ya rikoto ya fadi a rukunin wasu gidaje a Jihar Legas.

A sakon ta’aziyyarsa ga makusantan wadanda hatsarin na ranar Juma’a ya ritsa da su, shugaban ya ce Najeriya gaba daya na jiran hukumomin abin ya rataya wuyansu su gabatar da rohoton binciken.

Tuni Hukumar Binciken Hadarin Jiragen Sama (AIB) ta dauki akwatin daukar bayanan jirgin, bayan jami’an tsaro da na agaji sun dauke wadanda hatsarin ya ritsa da shu.

Hatsarin ya yi sanadiyyar mutuwar matukan jirgin mai saukar ungulu su biyu tare da jikkata mutum na uku da ke cikin jirgin wanda aka garzaya da shi asibiti.

Sakon da Kakakin Shugaban Kasa sa Femi Adesina ya fitar ya roka wa mamatan rahama ga da juriyar rashin ga ‘yan uwa da abokan arzikinsu da kuma samun sauki a kan kari ga wadanda suka samu rauni.

Hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu ya yi sanadiyyar mutuwar da wasu mutum biyu tare da jikkata wani a Jihar Legas.

Rahotanni na cewa jirign ya rikito ya fado a wani gida a layin Salvation a unguwar Opebi da ke Karamar Hukumar Ikeja.

Kakakin Hukumar Agaji ta Jihar Legas (LASEMA), Nosa Sokumba ya tabbatar da aukuwar hatsarin na ranar Juma’a wanda ya rutsa da jirgin kamfanin

“Tabbas jirgi mai saukar unugulu ya fado da misalin 12 na rana a Opebi. Jami’an LASEMA na kokarin ba da agaji a wurin”, kamar yadda aka ruwaito shi.

Janar Manajan Hukumar Olufemi Oke-Osanyintolu, ya ce an garzaya da mutumin da ya samu rauni daga hatsarin jirgin zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas.

“An yi wa hukumar kiran gaggawa cewa wani jirgi mai saukar ungulu na haya ya fada cikin wani gida …nan take muka fara shirin bayar da agaji.”, inji shi.