✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya dage tafiyarsa zuwa Landan

An dage tafiyar da aka shirya Buharin zai yi zuwa Landan a ranar Juma'a.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dage bulaguron da ya shirya yi zuwa birnin Landan domin duba lafiyarsa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun Fadar Shugaban Kasa, Femi Adesina, ya fitar  ranar Jumaa’a ta ce an dage tafiyar zuwa wani lokaci nan gaba.

Sanarwar ta ce sai nan gaba za a sanar da ranar da Shugaba Buharin zai tafi birnin na Landan.

Tun da farko, a ranar Juma’a ne aka tsara shugaban zai yi bulaguron.

Shugaba Buhari dai ya kasance mai yawan zuwa asibiti a Birtaniya domin duba lafiyarsa.