✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya dauki haramar tafiya Senegal

Tawagar Buhari ta kunshi wasu ministocin da manyan mukarraban Gwamnatin Tarayya.

Shugaba Muhammdu Buhari zai yi balaguro zuwa kasar Senegal ranar Talata domin halartar Taron Kasa da Kasa kan Harkokin Noma karo na biyu da za a gudanar a birnin Dakar.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa, Mista Femi Adesina ya fitar ranar Litinin.

Taron wanda shugaban Senegal kuma Shugaban Kungiyar Kasashen Afirka ta AU, Macky Sall zai karbi bakunci – an shirya shi ne domin samar da kyakkyawan yanayin noma domin ciyar da haniyar Afirka.

Mista Adesina ya ce maharta taron za su tattauna batun shigar da abinci da sauran kayan amfanin gona zuwa wasu kasashen, ciki har da Najeriya.

Ya kara da cewa yayin da nahiyar Afirka ke da mutum miliyan 249 da ke cikin kangin yunwa, taron – wanda Shugabannin Kasashen Afirka da ministocin kudaden da na noma na nahiyar, da kungiyoyin duniya za su halarta – zai saka aniyar kawar da yunwa a nahiyar Afirka nan da shekarar 2030.

Daga cikin tawagar da za ta yi wa shugaba Buhari rakiya zuwa taron har da Ministan Harkokin Kasashen waje, Geoffrey Onyeama, da Ministan Noma da Raya Karkara, Dakta Mohammad Mahmood Abubakar, da Mai Ba wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro Babagana Monguno da Daraktan Hukumar Tattara Leken Asiri, Ambassada Ahmed Rufai Abubakar.