✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya dawo Abuja bayan shafe kwana 4 a Habasha

Buhari ya dawo Abuja bayan shafe kwana hudu a Addis Ababa.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja da yammacin ranar Litinin, bayan shafe kwana hudu a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, inda ya halarci taron Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) karo na 35.

Shugaba Buhari ya isa filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja ne da misalin karfe 3:00 na rana.

Yayin da yake birnin Addis Ababa, Buhari ya halarci taruka daban-daban, ciki har da wani da Ministar Harkokin Wajen kasar Guinea Bissau, Suzi Barbosa, wacce ta yi masa bayani kan yunkurin juyin mulkin da aka yi a baya-bayan nan kan shugaba Umaru Sissoco Embalo.

Buhari, ya kuma gana da Fira-ministan kasar Habasha, Abiy Ahmed, inda suka tattauna kan ci gaban Afirka.

A yayin ganawar, shugaban da takwaransa na Habasha, sun amince da cewa bunkasa kasashen Afirka, na bukatar jagoranci mai karfi da hangen nesa, wanda zai biya bukatun jama’a.

Har wa yau, sun jadadda kafa cibiyoyin karfafa zaman lafiya wanda za su dinga samar da abubuwan da za su hana tashe-tashen hankula da juyin mulki a kasashen Afirka.