✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya dawo daga Landan bayan kwana 18

Daga a 2015 zuwa yau, Buhari ya shafe jimlar kwana 201 a kasar Burtaniya.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhar ya dawo Najeriya bayan ya shafe kwana 18 a birnin Landan na kasar Burtaniya.

Jirgin shugaban, kirar Air Force 1, ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe ne da ke Abuja da misalin karfe shida na yammacin ranar Juma’a.

Ya sami tarba daga Shugaban Ma’aikatan Fadarsa, Farfesa Ibrahim Gambari da Mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) da dukkan Manyan Hafsan Sojojin Najeriya da Babban Sufeton ’Yan Sanda da kuma Ministan Abuja.

Bayan saukarsa, shugaban ya kalli wani faretin ban-girma da sojojin kasa na Najeriya suka shirya masa, sannan kuma ya kalli wasu raye-rayen gargajiya.

Daga nan ne Shugaba Buhari ya hau wani jirgi mai saukar angulu inda ya wuce da shi Fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock da ke Abuja.

A ranar 26 ga watan Yuli ne dai Buhari ya bar Najeriya domin halartar wani taron kasa da kasa kan ilimi (GPE) na tsakanin shekarun 2021 zuwa 2025, kafin daga bisani kuma ya tsaya domin gana wa da likitocinsa a can.

Tun bayan zamansa Shugaban Kasa a 2015 dai, Buhari ya shafe jimlar kwana 201 a kasar Burtaniya domin halartar taruka da kuma ganin likitoci.

Ko a bana ma wannan ne karo na biyu da ya ziyarci kasar domin ganin likita, inda ya dawo ranar 30 ga watan Maris din da ya gabata bayan ya shafe mako biyu a can.Tun bayan zamansa Shugaban Kasa a 2015 dai, Buhari ya shafe jimlar kana 201 a kasar Burtaniya