✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya fadi adadin mutanen da aka kashe a zanga-zangar EndSARS

Gwamnatina ta yi tsayuwar daka wajen biyan bukatun masu zanga-zangar EndSARS.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce akalla rayukan mutum 69 ne suka salwanta a zanga-zangar nuna kin jinin cin zarafi da zaluncin rundunar ‘yan sanda ta SARS da ta mamaye kasar fiye da tsawon makonni biyu.

Daga cikin wadanda suka riga mu gidan gaskiya akwai farar hula 51, jami’an ’yan sanda 11 da kuma dakarun soji 7.

Shugaban kasar ya bayyana adadin rayukan da zanga-zangar ta yi sanadiyar salwantarsu a taron gaggawa da ya yi ta hanyar yanar gizo tare da tsofaffin shugabannin Najeriya cikin fadarsa a ranar Juma’a.

Ganawar Buhari ta tsoffin Shugabannin ta mayar da hankali ne wajen kawo karshen zangar-zangar da ta rikide zuwa tashin tashina musamman a wasu manyan birane na kasar da suka hada da Legas, Owerri, Kano da Abuja.

Buhari ya shaida wa tsoffin Shugabannin cewa gwamnatinsa ta yi tsayuwar daka wajen biyan bukatun masu zanga-zangar tare da cewa ba zai lamunci ganin marasa kishin kasa ba sun haifar da rikici a kasar.

Ya zuwa yanzu dai an samu lafawar zanga-zangar sai dai mutane da daman na zaman dar-dar a birane da dama yayin da rahotannin kwasar ganima da kai hari kan baki a yankin Kudu maso Gabas da Kudancin Kudu ke ci gaba da yaduwa.

Tsofaffin Shugabannin da suka amsa goron gayyatar sun hadar da Olusegun Obasanjo, da Ibrahim Babangida, da Goodluck Jonathan, da Abdulsalami Abubakar, da Yakubu Gowon da Earnest Shonekan.

Sauran mahalarta su ne Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo; da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha; da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari; da Mai Ba da Shawara kanHarkokin Tsaron Kasa, Babagana Monguno.