✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya fara aikin farfado da masana’antun Kano

Gwamnati ta ziyarci Jihar Kano da nufin farfado da masana’antun da suka durkushe

Gwamnatin Tarayya ta ziyarci Jihar Kano da zummar farfado da masana’antun da suka durkushe a jihar domin bunkasa tattalin arzikin kasa.

Ministan Masana’antu da Kasuwaci da Zuba Jari, Otumba Adeniyi ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci tawagar Ma’aikatarsa domin ziyartar Sarkin Kano, Mai Martaba Aminu Ado Bayero a fadarsa.

Ministan ta bakin Darektan Tsare-tsare na Ma’aikatar, Tijjani Babura ya ce Gwamnatin Shugaba Buhari ta fara farfado da masan’antu a fadin Najeriya domin samar da karin ayyukan yi da karin kudaden shiga.

Ya ce baya ga farfado da masana’antun gwamnati za ta kuma lura da gudanar da su duk da cewa tana fama da matsalar karancin kudade.

Da yake mayar da jawabi, Mai Martaba Sarin Kano ya bukaci tawagar Gwamnatin Tarayya da ta yi aikin cikin hanzari tare da tabbatar da aiwatar da sakamakon binciken da suka yi.

Sarki Aminu Ado Bayero ya jaddada muhimmancin farfado da masana’atun da ke Kano wajen habaka tattalin arziki a yankin Yammacin Afirka.