✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Buhari ya gabatar da kasafin 2022 na N16.39tn

Kasafin Naira tiriliyan 16.39 Buhari zai gabatar wa zauren Majalisar.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika wa babban zauren Majalisar Tarayya daftarin kasafin kudin 2022.

A jawabinsa na gabatar da daftarin kasafin na Naira tiriliyan 16.39, Buhari ya shaida wa zuaren majalisar cewa kasafin 2021 ya samu matsala, saboda Najeriya ta samu durkushewar tattalin arziki sau biyu, amma ta yi nasarar fitowa daga matsalar.

Ya ce a 2021 an samu kudaden shiga daga bangaren da ba na mai ba sun karu da kashi 7 cikin 100 a shekarar, amma kuma an gaza cimma hasashen kudaden shiga daga bangaren mai.

A cewarsa, annobar COVID-19 ta yi tasiri wajen raguwar man da aka hako.

Idan ba a manta ba, Majalisar Tarayya ta amince da kasafin 2022 zuwa 2024, a kan farashin gangan danyen mai Dala 57, sabanin Dala 40 na kasafin 2021.

Kasafin ya sanya farashin Dala a kan N410/$, hako gangar mai miliyan 1.88 a kowace rana a 2022, miliyan 2.23 a 203 da kuma miliyan 2.22 a 2024. Ya ce gibin Naira tiriliyan 5.01 da aka samu ta hanyar karbo rance.

Bayan gabatar da kasafin ne zai mika wa daftarin ga majalisar ta yi aikin tantance abin da ke kunshe a ciki gabanin amince da shi.

Gabanin amincewar majalisar, kwamitocinta za su bi diddigin abin da ke kushe ciki ta hanyar yi wa shugabannin hukumomi da ma’aikatu da cibiyoyin gwamnati game da abin da aka ware musu a kasafin.

Jami’an tsaro sun yi wa harabar Majalisar tsinke, inda suke tsaurara bincike a kan duk wanda da zai shiga ko ya fita daga harabar.

Wakilinmu ya lura cewa jami’an tsaron ba sa barin duk wanda ba shi da alamar izinin shiga wurin ya wuce.

Tun a ranar Laraba Buhari ya sanar da zaurukan majalisar – Majalisar Dattawa da ta Wakilai – cewa yana so ya gabatar musu da kasafin da misalin karfe 12 na ranar Alhamis.