✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Buhari ya fi shekara 40 yana zuwa Landan a duba lafiyarsa’

Buhari yana da halin a duba lafiyarsa a Landan.

Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Mista Femi Adesina, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya zarta shekaru 40 yana kai ziyara Landan domin a duba lafiyarsa.

Adesina ya ce Shugaban ya zabi a rika duba lafiyarsa a ketare saboda yana da ikon daukar nauyin hakan kari a kan mahanga ta ingatacciyar kiwon lafiya.

A halin yanzu, Shugaba Buhari yana Kasar Birtaniya inda zai halarci wani taron kasa-da-kasa kan Ilimi (GPE) sannan daga bisani ya wuce don ganin likitocinsa a birnin Landan.

A yayin da ba wannan ne farau ba, jam’iyyar adawa ta PDP ta soki tafiyar da shugaban ya yi zuwa birnin Landan, inda ta yi zargin cewa yana amfani da dukiyar talakawan Najeriya domin a duba lafiyarsa a ketare.

Sai dai yayin wata zantawa da ya yi da Gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba, Mista Adesina ya ce wannan ba shi ne karon fari ba da  shugaban ya yi balaguro zuwa katare domin a duba lafiyarsa.

A cewarsa, sama da shekara 40 tawagar likitocin da suka saba duba lafiyar shugaba Buhari har yanzu da su yake damawa kuma suna da cikakkiyar masaniya a kan lafiyar shugaban.

“A shawarce ya kamata Shugaba Buhari ya ci gaba kai wa wadannan likitoci ziyara domin su duba lafiyarsa kasancewar suna da duk wani tarihi a kan lafiyarsa.

“Kuma wannan shi ne dalilin da yake kai musu ziyara Landan domin su binciki lafiyarsa.

“Da tawagar wadannan likitoci shugaba Buhari yake mu’amala sama da shekara 40, saboda haka duk wani wanda yake da hali ya kamata ya ci gaba damawa da likitocin da suka san lafiyarsa ciki da waje.

Dangane da zargin da wasu gwamnonin PDP suka yi kan cewa Shugaba Buhari da mayar da Fadar Gwamnatin Najeriya tamkar hedikwatar jam’iyyar APC wajen gudanar da tarukan siyasa, Mista Adesina ya mayar musu da martani.

A cewarsa, gwamnatocin baya na jam’iyyar PDP da suka jagoranci kasar nan sun gudanar da tarukan siyasa a Fadar Gwamnatin kasar ta Aso Villa.

“Muna cikin wannan kasa lokacin da Shugaba Olusegun Obasanjao ya rika gudanar da tarukan majalisar amintattu ta jam’iyyar PDP.

“Haka zalika, muna cikin wannan kasa lokacin da Shugaba Yar’adua da Shugaba Jonathan suka rika gudanar da tarukan jam’iyyarsu a Fadar Villa, saboda mene ne abin magana don hakan ta kasance a yanzu, a cewar Adesina.