Buhari ya gayyaci Ministansa kan matsalar wutar lantarki | Aminiya

Buhari ya gayyaci Ministansa kan matsalar wutar lantarki

Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari
    Muideen Olaniyi da Abubakar Muhammad Usman

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gayyaci Ministan Lantarki, Abubakar Aliyu don tattauna yadda za a shawo kan matsalar karancin wutar lantarki da ake fama da ita a fadin Najeriya.

Kazalika, shugaba Buhari ya gayyaci gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma da mai ba shi shawara kan harkokin tattalin arziki, Farfesa Doyin Salami, don tattaunawa kan sha’anin tsaro a Kudancin kasar nan da kuma abin da ya shafi tattalin arziki.

Hadimin shugaban kasa, Garba Shehu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce Buhari zai gana da su da yammacin ranar Litinin a Fadar Villa da ke Abuja.
Shehu ya bayyana yadda shugaba Buhari ya yi Allah wadai da harin da wasu bata-gari suka kai kan ofishin ‘yan sanda a Jihar Imo.
Buhari ya shaida cewa dole ne a sake yin shiri na musamman kan yadda ake ci gaba da samun hare-hare a wasu sassan kudancin kasar nan.
Idan ba a manta ba a satin da ya gabata ne shugaba Buhari ya nemi afuwar ‘yan Najeriya kan yadda karancin wutar lantarki ke ci gaba da ta’azzara.