✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya gaza, ba ta mu yake ba —Yankin Arewa

Buhari bai damu da jama’ar Arewa, tsaronsu ko tattalin arzikin yankin ba —Dattawan Arewa

Kungiyar Al’ummar Arewacin Najeriya (CNG) ta jaddada goyon bayanta ga matsayin Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) cewa Shugaba Buhari ya gaza a babban aikinsa na samar da tsaro.

CNG ta ce a fili yake cewa Buhari ya kasa magance matsalar tsaro da ke ta’azzara a Arewa, don haka jama’ar yankin su tashi su kare kansu.

Ta ce, “Al’ummomin Arewa na fuskantar barazana daga ’yan bindiga da masu satar mutane, babu tsaro a manyan tituna, mazauna kauyuka na kauracewa, amma da gangan Shugaban Kasa ya ki yin abin da ya dace kuma ya ki bin shawarar galibin mutane cewa ya kori hafsoshin tsaro”.

Kakakin kungiyar Abdul-Azeez Suleiman, ya ci gaba da cewa: “Kullum abin da mutanenmu na karkara ke fada mana na da matukar ban kunya da tayar da hanakali.

“Yanzu mutane ba sa ma tunanin waiwayar batun noma saboda matsalar ta sa an kaurace wa kauyuka da gonaki.

“Wajibi ne yanzu dukkannin al’ummomin Arewa su hada kai su kare kansu saboda ’yan bindiga na tarwatsa mutanenmu daga gidajensu.

“Hatta a Jami’ar Ahmadu Bello da Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Nuhu Bamalli da ke Zariya babu aminci, a wannan lokacin da ake tunanin dalibai za su koma karatu.

“Hakan ya karya wa iyaye gwiwa cewa kada su tura ’ya’yansu zuwa makaranta har sai sun tabbatar da cewa za a kare rayukansu”, inji Suleiman.

 

Arewa ta fusata da Buhari kan rashin tsaro

A ranar Litinin kungiyar ACF ta bayyanna takaici da bacin ranta saboda karuwar rashin tsaro a Arewa a mulkin Buhari.

Sakataren Yada Labaran ACF na Kasa, Emmanuel Yewa, ya ce ’yan Arewa ba su taba zaton Gwamnatin Buhari za ta ba da kunya ba.

“Gwamnatin ba ta daukar matakan dakile aukuwar matsalar, saboda haka ya kamata ta rika aiki da rahotannin bayanan sirri da take samu.

“Ta sha fada mana ta ’yanta hanyar Kaduna-Abuja amma bayan dan lokaci sai a kara kai wani kazamin hari a kan hanyar.

“Ba sa tara bayanan sirri yadda ya kamata shi ya sa ’yan bindiga da mayakan Boko Haram suke shan gabansu”, inji shi.

ACF ta ci gaba da cewa: “Mun san gwamnatin da ta shude ta dagula lamarin matsalar tsaro, amma shugaban lokacin ba masanin harkar tsaro ba ne, malamin jami’a ne ya shiga siyasa har ya tsinci kansa a matsayin shugaban kasa.

“Shugaba Buhari mai mai ci kuwa, ya yi yakin basasa sannan shi ne Kwamandan da ya fatattaki sojojin Chadi da suka taba kutse a Najeriya a zamanin Gwamnatin Shagari, don haka yana da duk abin da ake bukata don magance matsalar”, a cewarsa.

 

Matsalar Arewa ba ta dami Buhari ba —NEF

A nata bangaren, Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta ce babu ko tantanma cewa Gwamantin Buhari ba ta damu da jama’ar Arewa ba ballanta abin da ya shafi tsaronsu ko tattalin arzikin yankin.

A martaninta ga sabon wa’adin da gwamantin ta sanar na kammala aikin titin Kano-Abuja a shekara biyar masu zuwa, Kakakin NEF, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce rashin saurin aikin ya sa babbar hanyar ta zama mafi hadari a fadin Najeriya.

Bugu da kari, ya ce kara lalacewar hanyar na ba wa masu satar mutane damar cin karensu babu babbaka a kan hanyar inda ake ta asarar rayuka da biliyoyin Naira.

 

Fadars Shugaban Kasa ta yi gum

Kakakin Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu, bai amsa sakon da wakilinmu ya aika masa ba.