✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya haramta tashi da saukar jirage a Zamfara

Haka kuma, ya amince babu wani jirgi da zai kara sauka ko tashi daga Jihar Zamfara.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin haramta tashi da saukar jirage a Jihar Zamfara nan take.

Mai bai wa Shugaban Kasar Shawara kan Harkokin Tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno ne ya sanar da hakan a ranar Talata yayin ganawa da manema labarai bayan kammala zaman Majalisar Tsaro da ya wakana a fadar Shugaban Kasar da ke Abuja.

Babagana Monguno ya ce Shugaban Kasar ya kuma ba da umarnin haramta hakar ma’adanai a Jihar ta Zamfara da zummar magance ayyukan ta’addanci.

“A bisa shawarwarin da muka bai wa Shugaban Kasa, ya bayar da umarnin haramta duk wasu ayyuka na hakar ma’adanai a Jihar Zamfara har sai yadda hali ya yi”.

“Haka kuma, ya amince babu wani jirgi da zai kara sauka ko tashi daga Jihar Zamfara.”

Zaman Majalisar Tsaron da Shugaba Buhari ya jagoranta kuma aka shafe awanni biyar ana gudanarwa a babban dakin taro na Council Chambers da ke fadarsa, ya samu halarcin Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da kuma Shugaban Ma’aikatar Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Sauran mahalartan sun hada da Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi; Ministan Harkokin ’Yan sanda, Maigari Dingyadi, Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, da Manyan Hafsoshin Soji da kuma Babban Sufeton ’Yan sanda, Muhammad Adamu.