✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya jajanta kan mutuwar Hajiya Ladi Gumel

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa Shugabar Kwamitin Wasannin Olympics na Najeriya, Injiniya Habu Ahmed Gumel, bisa rasuwar matarsa, Hajiya Ladi Gumel. Shugaba Buhari,…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa Shugabar Kwamitin Wasannin Olympics na Najeriya, Injiniya Habu Ahmed Gumel, bisa rasuwar matarsa, Hajiya Ladi Gumel.

Shugaba Buhari, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba, ya kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalai, makunsanta da dukkanin dangin Hajiya Ladi Gumel.

Bayan neman da su dauki dangana, Buhari ya bukaci masoya da ’yan uwan marigayiyar da su yi koyi da kyawawan dabi’unta tare da neman su da yin alfahar da shaidar rayuwa ta gari da ta samu wajen kyautata alakarta da Mahallicinta.

Shugaban ya yi addu’ar neman Allah Ya jikan ta da Rahama tare da bai wa iyalanta juriyar rashin da suka yi.

Hajiya Gumel mai shekaru 56 ta mutu ta bar ’ya’ya hudu bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya.