✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kaddamar da aikin Tashar Jirgin Kasa a Legas

Shugaba Buhari ya kai ziyara Jihar Legas ce a ranar Alhamis.

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya isa birnin Ikko inda ya kaddamar da aikin layin dogo wanda zai tashi daga Legas zuwa Ibadan.

Buhari ya kaddamar da sabon aikin layin dogo wanda gwamnatinsa ta kammala mai tsawon kilomita 157 a tashar Jiragen Kasa ta Mobolaji Johnson da ke Ebutte Metta.

Kazalika, shugaba Buhari zai kaddamar da aikin tashar Jiragen Ruwa ta Energy Nature Light Terminal a Tashar Apapa, a wani yunkuri na ci gaba da kaddamar da ayyukan tabbatar da tsaro na sufurin jiragen ruwa da ake kira Deep Blue Project.

Tashar Mobolaji Johnson
Cikin Tashar Mobolaji Johnson da Shugaba Buhari ya kaddamar
Daya daga cikin fuskokin Tashar Mobolaji Johnson
Kewaye da kuma harabar Tashar Mobolaji Johnson da Buhari ya kaddamar

A tashar ta Apapa, Shugaba Buhari ya kaddamar da jiragen sintiri na ruwa da na sama da kuma masu saukar ungulu, wadanda za su rika shawagi a teku domin magance matsalar ’yan fashi da sauran ayyukan laifi a tekun Najeriya.

Tare da Shugaban akwai Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo Olu da takwarorinsa na Oyo da Ekiti, Seyi Makinde da Kayode Fayemi.

Haka kuma, akwai Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola da wasu manyan jami’an gwamnati.