✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya kaddamar da sabbin jiragen yaki

Rundunar Sojin Sama na jiran isowar karin jirage 20 kafin karshen 2021.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya kaddamar da sabbin jiragen yaki kirar JF-17 ga Rundunar Sojin Sama ta Najeriya.

An kaddamar da jiragen ne a Barikin Sojin Sama da ke Makurdi, a yayin bikin cikar Rundunar shekara 57 da kafuwa.

“Wannan ya nuna yadda aka samu ci gaba tsawon shekara 57, ta hanyar kare martabar kasar nan daga matsalolin tsaro da kai dauki daga sama.

“Kaddamarwa na da matukar muhimmanci a wajena, saboda na cika wani bangare na alkawarin da na dauka na samar da kayayyakin yaki ga Rundunar Sojin kasar nan,” inji Buhari, wanda Ministan Tsaro, Bashir Magashi ya wakilta.

Ya kara da cewa ce yana da yakinin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya za ta ci gaba da yaki da ta’addanci a fadin kasar.

Kazalika, ya jinjina wa daukacin mutanen kasar da suka tsaya kai da fata wajen ganin Najeriya ba ta rabu ba.

Sannan ya ja hankalin ’yan Najeriya da su ajiye bangaranci, kabilanci da bambamcin addini da ke tsakaninsu, don tafiya tare, a tsira tare.

A nasa bangaren, Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Oladayo Amao, ya bayyana cewa Rundunar tana sa ran karin jirage 20 daga yanzu zuwa cikin watan Yulin mai kamawa.

“Ina sanar da ku cewa tun bayan karbar wannan gwamnati mun samu manyan jirage guda 23, wanda 10 daga cikinsu na musamman ne, sai kuma jiragen yake 13.

“Daga cikin wadanda muka samu akwai jiragen yaki kirar JF-17, MI-35M, sa kuma helikwafta, kuma dukkaninsu an same su ne a kasa da shekara shida,” cewar Amoa.