✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kaddamar da titin Kano zuwa Maiduguri

Gwamnatin Buhari ta bayyana aniyarta na samar da kayan more rayuwa da saukake harkokin kasuwanci

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sashe na biyu na babban titin Kano zuwa Maiduguri, Shuwarin zuwa Azere da kuma Dutse zuwa Kwanar Huguma, a jihohin Jigawa da Bauci.

Buhari wanda Ministan Ruwa, Suleiman Adamu, ya wakilta a wurin kaddamar da titin ya jaddada aniyar gwamnatinsa a bangaren samar da abubuwan more rayuwa da saukaka yin harkokin kasuwanci, wanda hakan na daga cikin dalilin kammala ayyukan da ta gada da kuma wadanda ta faro.

“Gwamnati ta shigo karshen wa’adinta, muna kuma kokarin kammala manyan ayyuka,” inji Ministan a lokacin da yake bayani a ranar Litinin.

“Gwamna Muhammadu Badaru ya lissafo ayyukan titi da dama da ake kan aiki a kansu domin kammalawa da suka hada da Kwanar Dumawa zuwa Babura da Babban Mutun zuwa Gaya zuwa Jahun zuwa Kafin Hausa.

“Akwai kuma aikin titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi da ya hade da Dutse; Ina kuma amfani da wannan dama in sanar da gwamna cewa an fara aikin mayar da titin Kano zuwa Kwangala mai hannu biyu.

“A yau muna mika titin nan mai tsawon kilomita 131.8 wanda shi ne sashe na biyu na titin Shuwarin zwau Azare da kuma Kano zuwa Maiduguri wanda ya hada da Dutse zuwa Kwanar Huguma,” inji shi.

A shekarar 2006 aka bayar da aikin titin Shuwarin zuwa Azare a kan biliyan N35.8 a kan wa’adin wata 40.

Daga baya aka kara kudin zuwa biliyan N65.3 aka kuma kara wa’adin zuwa watan Yunin 2021, bayan an kara kilomita 30.5 daga Dutse zuwa Kwanar Huguma da sauran wasu abubuwa.