✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kadu da mutuwar sarauniyar kyau

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna kaduwa tare da alhininsa biyo bayan mutuwar tsohuwar Sarauniyar Kyau Ibidun Itua-Ighodalo, mai dakin Shugaban Cocin Tiriniti da ke…

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna kaduwa tare da alhininsa biyo bayan mutuwar tsohuwar Sarauniyar Kyau Ibidun Itua-Ighodalo, mai dakin Shugaban Cocin Tiriniti da ke Legas, Fasto Itua Ighodalo.

A sanarwar da Mai Taimaka wa Shugaba Buhari a kan Harkokin Yada Labarai da Al’amuran Hulda da Jama’a Femi Adesina ya fitar a ranar Lahadi, 14 ga watan Yuni, ya ce Shugaba Buhari ya girgiza da mutuwar, inda ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayiyar da kuma daukacin mambobin cocin na Tiriniti.

Sanarwar ta ce Shugaba Buhari yana sane da cewa Fasto Ighodalo na cikin mutanen da ke yi wa Najeriya addu’a kuma ya aike masa da sakon ta’aziyya a lokacin da tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati, Malam Abba Kyari ya rasu.

“Muna fatan za ku karbi ta’aziyyarmu, Allah Ya ba ku hakurin jure wannan rashi, Ya ba ku kwarin gwiwa a wannan lokaci da Ya jarabce ku”, inji sanarwar.