✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kadu da rasuwar Sama’ila Funtua

Rasuwar Isma’ila Isa Funtua ta bar babban gibi mai wuyar cikewa a rayuwar Buhari.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce rasuwar Malam Isma’ila Isa Funtua ta bar babban gibi mai wuyar cikewa a rayuwarsa.

Buhari ya bayyana matukar kaduwa da rasuwar na hannun daman nasa wanda ya rasu dare Litinin sakamakon bugun zuciya a Abuja.

“Tsohon abokin nasa ya kasance tare da shi a tsawon fadi-tashin siyasar da ya yi” inji sakon ta’aziyyar da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar.

Buhari ya kuma yi addu’ar Allaha Ya jikan Isma’ila Funtua ya kuma ba wa iyalansa da masoya da abokan aiki hakuri da dangana.

Ya bayyana mamacin a matsayin dattijo kowa ke girmamawa wanda kuma rasuwarsa babbar rashi ce musamman ga fannin aikin jarida a Njariya da ma duniya baki daya.

Marigayri Isma’ila wanda ya bar duniya yana da shekaru 78 da haihuwa, tsohon minista ne kuma tsohon shugaban kungiyar mawallafa jaridu ta Najeriya (NPA),

Shi ne kuma shugaban babban kamfanin gine-gine na bullet wanda ya gina kafafarun gine-ginen gwamnati a Abuja.