✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kadu da rushewar bene a Legas

Buhari ya bayyana damuwa kan yawaitar samun rushewar gine-gine a kasar.

Shugaba Buhari ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su yi aiki kafada da kafada da kwararru domin kawo karshen rushewar gine-gine a kasar nan.

Shugaban ya yi kiran ne ranar Litinin a wata sanarwa da Fadar Gwamnatin Najeriya ta fitar biyo bayan rushewar wani bene a Unguwar Enute Metta da ke Jihar Legas, inda har yanzu jami’an agaji ke ci gabaa da aikin ceto.

Sanarwar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana takaicinsa kan yadda ake yawaitar samun rushewar gine-gine a kasar nan.

Shugaban kasar ya kuma mika jaje ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, tare da yaba wa wadanda suka ba da agajin gaggawa gare su kama daga jami’an gwamnati har zuwa al’ummar gari.