✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kafa kamfanin samar da ababen more rayuwa

Kamfanin mai suna Infra-Co zai fara aiki da jarin Naira tiriliyan daya

Shugaba Buhari ya amince da kafa kamfanin samar da ababen more rayuwa mai suna Infra-Co wanda zai fara aiki da jarin Naira Tiriliyan daya.

Kakakin Shugaban Kasa, Laolu Akande ya sanar cewa Infra-Co wanda zai kasance da hadin gwiwar kamfanonin zai dauki nauyin bunkasa kadarorin gwamnati, gina su da kuma gyaran su.

Ya ce kamfanin zai kuma sanya kudade domin wajen rage karancin abubuwan more rayuwa da suka hada da hanyoyi, layukan dogo, wutar lantarki da sauran muhimman bangarori.

Ya kara da cewa an kirkiri kamfanin da dabaru daga Hukumar Tattalin Arzikin Kasa (NEC) da Babban Bankin na Najeriya (CBN).

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne kuma zai shugabanci Kwamitin Gudanarwa da aka dorawa alhakin kafa kamfanin da ake tunanin zai bunkasa zuwa Naira tiriliyan 15 na kadarori da jari a nan gaba.

Ya ce asalin zuriya ga kamfanin zai fito ne daga Babban Bankin Najeriya, Hukumar Kula da Zuba Jari ta Nijeriya, NSIA, da kuma Kamfanin Kudin Afirka.

Ya ce Kwamitin Infra-Co wanda Gwamnan Babban Bankin zai jagoranta, ya hada da Manajan-Daraktan Hukumar Kula da Zuba Jari ta Najeriya, Shugaban Kamfanin Kudi na Afirka, da wakilan Kungiyar Gwamnonin Najeriya, da Ma’aikatar Kudi, Kasafin Kudi da Tsarin Kasa.

Laolu ya ce kwamitin zai kuma samu daraktoci masu zaman kansu uku daga kamfanoni masu zaman kansu.

Ya ce don magance matsalar gibin kayayyakin more rayuwa a Najeriya, Gwamnatin Buhari na ci gaba da binciko sabbin hanyoyin samar da kudade kamar su PIDF wanda aka tsara don samar da Gadar Neja ta biyu, Babban titin Abuja-Kaduna-Zaria-Kano, da sauran ayyuka.