✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kafa kwamitin rage radadin talauci a Najeriya

A baya bayan nan ne Bankin Duniya ya ce ’yan Najeriya miliyan bakwai sun fada cikin talauci.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani kwamiti na musamman domin rage radadin talauci a tsakanin al’ummar kasar tare da bijiro da dabarun bunkasa tattalin arziki.

Cikin wata sanarwa da Femi Adesina, Mai Magana da Yawun Shugaban ya fitar a ranar Talata, an bayyana Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin jagoran kwamitin.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Sakataren Gwamnatin Tarayya da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa da gwamnonin jihohin Ekiti Ekiti da Delta da Sakkwato da  Borno da Nasarawa da Ebonyi da suke wakiltar shiyyoyin siyasar Najeriya guda shida.

Adesina ya ce Shugaban ya sake jaddada kudurinsa na cire mutum miliyan 100 daga bakin talauci cikin shekara 10 bisa kyakkyawan tsarin yadda za a alkinta da samar wa shirin kudaden gudanarwa.

“Idan kasar Indiya za ta iya fidda mutum miliyan 271  daga kangin talauci tsakanin shekarar 2006 zuwa 2016, to tabbas Najeriya ma za ta iya fidda mutum miliyan 100 daga kangin fatarar cikin shekaru goma.

‘’Abin farin ciki a nan shi ne mun riga mun fara shirin amma akwai bukatar mu kawar da kalubalen da ke tattare da aiwatar da shirin da ma zabo mutanen da ba dace ba tare da karancin kudaden gudanar da shirin,’’ kamar yadda Shugaban Kasar ya nuna.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin ya ce matsayar Shugaba Buhari kan shirin shi ne gwamnatocin Kananan Hukumomi da Jihohi da na Tarayya su yi aiki kafada da kafada wajen yaki da talaucin a cikin kasa.

Ana iya tuna cewa, cikin rahoton da Bankin Duniya ya fitar a baya-bayan nan, ya ce hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya na kara talaucin da kuma tabarbarewar harkokin kasuwanci.

Bankin ya ce kimanin ’yan Najeriya miliyan bakwai ne suka fada cikin talauci a shekarar 2020 saboda tashin farashin kawai.