Buhari ya karbi bakuncin shugaban Nijar, Bazoum a Abuja | Aminiya

Buhari ya karbi bakuncin shugaban Nijar, Bazoum a Abuja

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohammed Bazoum
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohammed Bazoum
    Sani Ibrahim Paki

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin takwaransa na Jamhuriyar Nijar, Mohammed Bazoum a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja.

Bazoum ya sauka ne da misalin 1:22 na ranar Litinin domin ziyarar da ake sa ran zai shafe kwanaki biyu a Najeriya.

Daga cikin wadanda suka tarbi shugaban akwai Shugaban Ma’aikatan Shugaba Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari da Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Muhammd Bello da wasu mukarraban Shugaban Kasar.

Shugaba Buhari da takwaransa Bazoum a Fadar Aso Rock ta Abuja

Kazalika, Gwamnonin jihohin Sakkwato da Borno da Yobe da Kebbi da Zamfara suma suna Fadar Shugaban domin tarbar shugaba Bazoum, wanda aka rantsar ranar biyu ga watan Afrilun 2021 domin wa’adin shekaru biyar.

Jim kadan da kammala dan kwarya-kwaryar bikin karbar tasa ne Shugabannin biyu suka sa labule domin tattaunawa.

Mai kimanin shekaru 61 a duniya, ana sa ran Bazoum zai yi bude-baki da Shugaba Buhari da misalin karfe 6:50 na yamma.