✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kashe tiriliyan N1.8 kan manyan ayyuka a 2020

Naira biliyan 118.3 sun tafi wurin manyan ayyukan yaki da COVID-19

Gwamntin Tarayya ta kashe Naira tiliyan 2.8 wurin aiwatar da manyan ayyuka a shekarar 2020.

Ministar Kudi da Tsare-tsaren Kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a yayin kaddamar da kasafin kudin 2021 a Abuja ranar Talata.

Da take bayani a taron da aka gudanar ta bidiyo, Ministar ta ce kashi 89% na kudaden an kashe su ne a kan manyan ayyuka.

Sai dai ta yi bayani cewa Naira biliyan 118.3 kuma an kashe su ne a kan manyan ayyukan yaki da annobar COVID-19.

Ta ce a shekarar 2020, Najeriya ta kashe tiriliyan N3.27 wurin biyan basuka, sai kuma tiriliyan N3.19 da aka kashe wurin biyan albashi da fansho a shekarar ta 2020.