Buhari ya kori Shugaban Hukumar Samar da Ayyuka | Aminiya

Buhari ya kori Shugaban Hukumar Samar da Ayyuka

Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari
    Sagir Kano Saleh da Idowu Isamotu

Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami Darakta-Janar na Hukumar Samar da Ayyyuka ta Kasa (NDE), Nasir Muhammad Ladan Argungu daga mukaminsa.

Wani babban jami’in hukumar ta NDE ya tabbatar wa Aminiya cewa an umarci Minista a Ma’aikatar Kwadago da Daukar Aiki, Festus Keyamo ya nada Darakta-Janar na riko daga cikin Manyan Daraktocin hukumar.

Ba a dai bayyana dalilin sallamar Nasiru Ladan daga mukaminsa ba, amma majiyarmu ta ce ba zai rasa nasaba ba da tafiyar hawainiya a daukar ma’aikata 774,000 daga kananan hukumomin Najeriya 774.