✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya mika karin kasafin biliyan N895 ga Majalisa

Za a yi amfani da kudaden wajen sayen makamai da allurar rigakafin COVID-19

Shugaba Buhari ya gabatar da bukatar karin kasafain kudi na biliyan N895 ga Majalisar Tarayya domin amincewarta.

Shugaban Kwamitin Sojan Kasa a Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume ne ya bayyana hakan ranar Juma’a a Abuja bayan ganawar sirri tsakaninsa da Babban Hafsan Sojan Kasa, Manjo-Janar Farouk Yahaya.

Sanata Ndume ya ce: “Shugaban Kasa ya ba mu tabbacin zai sake fasalta hukumomin tsaro; Bukatar karin kasafin kudin tana nan a gabanmu kuma za mu yi gaggawar amincewa da ita.”

Da yake magana bayan tabbatar da shi a mukamin Babban Hafsan Sojin Kasa, Manjo-Janar Farouk Yahaya ya ba da tabbacin cewa dakarun rundunar za su ci gaba da bayar da gudummawarsu ta fuskar dakile matsalolin tsaro a kasar nan.

A ranar Laraba Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da daftarin karin biliyan  N895 na kasafin kudin 2021 domin sayo makamai da kuma allurar  rigakafin COVID-19.

Ministar Baitul Mali da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta ce daftarin ya kunshi  biliyan N770.6 da za a kara karfafa rundunonin tsaro domin tunkarar kalubalen da ake fuskanta a Najeriya a halin yanzu.

Biliyan N83.56 kuma an tanadar da shi ne domin sayowa da ma jigilar allurar rigakafin COVID-19 daga kamfanin Johnson and Johnson.