✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya mika wa Majalisa kasafin tiriliyan 2.557 don biyan tallafin man fetur

Buhari na neman majalisar ta amince da karin fiye da naira tiriliyan biyu da rabi a kasafin kudin bana.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika wa Majalisun Dokokin Kasar bukatar kara Naira Tiriliyan 2.557 a Kasafin Kudin Kasar na bana 2022 domin biyan tallafin man fetur.

Aminiya ta ruwaito cewa, Fadar Gwamnatin Najeriya ta mika wa Majalisun Tarayyar bukatar ce a ranar Talata domin domin tarar hanzarin biyan tallafi man fetur da aka yanke shawarar ci gaba da biyan dillalan man fetur a kasar.

Bukatar neman gyaran ta biyo bayan dakatar da Dokar Man Fetur (PIA) ce, wadda ta tanadi a soke biyan tallafin man fetur din da kuma mayar da hada-hadar mai ta ’yan kasuwa zalla.

Wannan na kunshe ne cikin wata wasika da shugaban ya rubuta wa ’yan majalisar wadda kuma Shugaban Majalisa Sanata Ahmad Lawan da Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila suka karanta a zaurukan majalisunsu.

A halin yanzu dai gwamnati na neman majalisar ta amince da karin fiye da naira tiriliyan biyu da rabi (triliyan N2.557) don biyan kudin tallafin mai daga Yuli zuwa Disamban 2022 da kuma sake duba Dokar Kudi ta Finance Act 2021.

A cikin wasikar, Buhari ya ce gyaran ya zama dole don kara wasu ayyuka a ciki da suka hada da tallafin man fetur, wanda tun farko gwamnatinsa ta yi niyyar daina biya kafin daga baya ta sauya shawara.

Tun da farko gwamnati ta tanadi kudin tallafin na wata shidan farko na shekarar 2022 a kasafin kudin, inda aka ware biliyan N443 daga Janairu zuwa Yunin 2022.