✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya murkushe Boko Haram a Najeriya —Buratai

Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya Laftanar-Janar Yusuf Tukur Buratai mai ritaya ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya cika alkawarin da ya dauka…

Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya Laftanar-Janar Yusuf Tukur Buratai mai ritaya ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya cika alkawarin da ya dauka ranar 29 ga watan Mayun 2015 na kawo karshen ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP.

Buratai ya bayyana hakan ne a ganawarsa da manema labarai a Abuja, inda ya ce kuskure ne babba mutane su dinga tunanin daina jin duriyar kungiyoyin baki daya shi ne ke nufin an kawo karshensu.

Ya ce hanyar da kadai za a iya cimma hakan ita ce idan ’yan ta’addan sun amince da watsi da mummunan tunaninsu, da kuma rungumar tsarin Dimokuradiyya, hadi da martaba kundin tsarin mulkin Najeriya da zaman lafiya.

Buratai ya ce tun daga hawan Buhari mulki yake da manufofi da tsare-tsaren kawo karshen ’yan  ta’addan, da kuma dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya baki daya.

Kazalika ya ja hankalin ’yan Najeriya cewa wani fitaccen masani Philp H. Gordon ya ce nasarar sojoji a yaki ba shi ke kawo karshen ta’addanci ba a ko’ina a duniya.

“Sakaci, rashin hada kai da wadanda suka kamata da kuma shigar da dabarun yaki da Boko Haram na son kai, ya sa ’yan ta’addan suka kawo matsayin da suke yanzu.

“Kuma shugaban kasa ya fito karara ya fadi inda matsalolin suke musamman a bangaren jami’anmu na ’yan sanda, da kuma gaskiyar cewa ’yan Boko Haram da ISWAP ba Musulman gaskiya ba ne,” in ji shi.

Buratai ya yi alkawarin yin cikakken bayani kan matakai da yadda sojoji suka fatattaki ’yan ta’addan a littafinsa da yake rubutawa, ko ’yan Najeriya sa yi wa kansu alkalanci.