✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya nada dan shekara 40 a matsayin sabon Shugaban EFCC

Nadin sabon shugaban Hukumar EFCC na zuwa ne watanni bayan sauke Ibrahim Magu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Abdulrasheed Bawa a matsayin sabon shugaban Hukumar EFCC mai hana yi wa tattalin arziki kasa ta’annati.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Mista Femi Adesina ya fitar ranar Talata ta ce Mista Bawa mai shekaru 40 a duniya, yana da kwarewa a fannin binciken zamba da almundahana da halalta kudin haram da sauran laifuka da suka shafi yi wa tattalin arziki zagon kasa.

Sanarwar ta ce Mista Bawa yana da shaidar digiri na farko a fannin tsimi da tanadi da kuma shaidar digiri na biyu a nazarin huldar kasashen waje da diflomasiyya.

Nadin Abdulrasheed Bawa a matsayin sabon shugaban Hukumar EFCC na zuwa ne watanni bayan sauke Ibrahim Magu, wanda har yanzu ake zarginsa da aikata laifuffuka irin wadanda aka dora masa nauyin yaki da su.

A wasikar neman tabbatar da shi da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Kasar ya ce wannan nadi ya yi daidai da tanadin dokokin Hukumar ta EFCC.