✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya nada Dangote ya jagoranci kwamitin dakile Maleriya a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce nada attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote a matsayin shugaban kwamitin dakile cutar Maleriya na kasa (NEMC). Buhari, ya ce…

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce nada attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote a matsayin shugaban kwamitin dakile cutar Maleriya na kasa (NEMC).

Buhari, ya ce ya nada shi ne la’akari da dimbin gudunmawarsa a bangaren lafiya a nahiyar Afirka baki daya.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da kwamitin mai mutane 16 ranar Talata, inda ya ce nasararsu a aiwatar da shirin za ta taimaka wajen rage abin da cutar ke lakumewa daga tattalin arzikin Najeriya da kusan Naira biliyan 687 a shekarar 2022, da kuma Naira tiriliyan biyu nan da shekarar 2030.

Shugaban ya kuma sanar da kwamitin cewa baya ga inganta lafiya, shirin zai amfani zamantakewa da tattalin arzikin kasar.

Sauran ‘yan  kwamitin sun hada da Shehu Ibrahim a matsayin Sakatare da Mataimakin Shugaban kasa kan harkokin siyasa da tattalin arziki, sai Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi da kuma Sanata Yahaya Oloriegbe.

Haka zalika, akwai irinsu Shugaban Kwamitin Lafiya na majlisa Abubakar Dahiru, da shugaban Kwamitin Majalisar na yaki da cutar sida, tarin fuka, da Maleriya Dokta Ehanire da Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Mahmuda Mamman.

Har wa yau, kwamitin ya kuma kunshi Shugabar Daraktocin bankin UBA, Folurunsho Alakija, da attajiri Tony Elumelu, da Shugabar Kamfanin Sharon Rose, da shugaban Bankin Access Herbert Wigwe sai Femi Otedola da ke shugabantar gidan man Forte.

Haka kuma akwai Shugabar Majalisar Kungiyoyin Mata, Hajiya Lami Lau da John Cardinal Onaiyekan, sai Shugabar Kungiyar Mata Musulmi ta Kasa (FOMWAN), Alhaja Amira Rafayat Sanni da Dokta Erpetua Uhomoibhi wanda ke jagoranatr shirin kawo karshen cutar Maleriya na NEMP.