✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya nada Farfesa Duna sabon Daraktan NBRRI

Farfesa Duna ya yi godiya tare da alkawarin kawo sabon sauyi a cibiyar.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Farfesa Samson Duna a matsayin sabon Daraktan Hukumar Gina Gidaje ta Kasa da Binciken Ingancin Gine-Gine da Hanyoyi (NBRRI).

Ministan Kimiyya da Fasaha Dakta Ogbonnaya Onu ne ya gabatar da takadar shaidar nadin ga Farfesa Samson Duna a madadin shugaba Buhari.

Sanarwar nadin sabon Shugaban Hukumar NBRRI ta zo ne a ranar Laraba, 23 ga watan Dasimban 2020.

Da ya ke jawabi bayan karbar takaidar shaidar nadin, Fafesa Duna ya ce, “Na yi alkawarin kawo sabon sauyi a NBRRI, don kawo ci gaba ga kasa baki daya,” cewar Duna.

Farfesa Duna, ya ce zai yi aiki tukuru domin ciyar da cibiyar da ma kasa baki daya.

Duk da cewa an haife shi a ranar 13 ga watan Maris, 1968 a Katsina-Ala dake jihar Benuwai, Farfesa Duna ya fito ne daga karamar hukumar Billiri ta jihar Gombe.