Buhari ya nada Mohammed Hassan Abdullahi Ministan Muhalli | Aminiya

Buhari ya nada Mohammed Hassan Abdullahi Ministan Muhalli

Mohammed Hassan Abdullahi
Mohammed Hassan Abdullahi
    Ishaq Isma’il Musa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mohammed Hassan Abdullahi a matsayin sabon Ministan Muhalli.

Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ne ya bayyana nadin nasa a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce: “Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nada Mohammed H. Abdullahi a matsayin sabon Ministan Muhalli daga ranar 6 ga Afrilu, 2022.”

Mohammed Hassan Abdullahi wanda lauya ne kuma dan asalin Jihar Nasarawa, shi ne Karamin Minista Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha kafin nada shi babban minista.