✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya sauya ministoci, ya rantsar da sabbi

Ya rantsar da sabbin minsitoci sa'o'i kadan bayan ’yan bindiga sun kai hari a Gidan Yarin Kuje da ke Abuja.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada sabbin minsitoci, sa’o’i kadan bayan ’yan bindiga sun kai wa ayarin motocinsa hari a mahaifarsa, Daura.

Nade-naden na zuwa ne sa’o’i bayan wani hari da aka kai wa Gidan Yarin Kuje da ke Abuja, inda mahara suka saki fursunoni akalla 600, ciki har da mayakan Boko Haram da ’yan bindiga.

Ya sauya wa ministoci biyar ma’aikatu tare da bayyana ma’aikatun da sabbin ministocin na ya nada za su jagoranta.

Ministocin da ka yi wa sauyin ma’aikatun su ne:

  • Umana Okon Umana, Ministan Neja Delta
  • Gbemisola Saraki, Minista a Ma’aikatar Hakar Ma’adinai
  • Dokta Olorunimbe Mamora, Ministan Kimiyya da Fasaha
  • Sharon Ikeazor, Minista a Ma’aiktar Neja Delta
  • Muazu Jaji Sambo, Ministan Sufuri.

Sabbin ministocin da ma’aikatatun da aka ba su kuma:

  • Umar Ibrahim El yakub – Minista a Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje
  • Goodluck Nanah Opiah – Minista a Ma’aikatar Ilimi
  • Ekumankama Joseph Nkama – Minista a Ma’aikatar Lafiya
  • Ikoh Henry Ikechukwu – Minista a Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha
  • Odum Udi –  Minisat a Ma’aikatar Muhalli
  • Ademola Adewole Adegoroye – Minista a Ma’aikatar Sufuri.

Buhari ya sanar da sauye-sauyen ne a zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya a Fadar Shugaban Kasa ranar Laraba.

A lokacin zaman ne ya rantsar da sabbin ministocin bayan Majalisar Dattawa ta tantance su a makon jiya.

Rukunin farko na sabbin ministocin da ya rantsar su ne: Henry Ikechukwu Ikoh (Abia) da Umana Okon Umana (Akwa Ibom) da Odum Odih (Ribas) da kuma Ademola Adewole Adegoroye (Ondo).

Na biyun kuma su ne: Umar Ibrahim El-Yakub (Kano) da Goodluck Nnana Opiah (Imo) da kuma Egwumakama Joseph Nkama (Ebonyi).

Kafin rantsarwar taron ya yi shiru na minti daya domin nuna jimamin rasuwar Sakatare-Janar na Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Mai (OPEC) mai barin gado, Muhammad Barkindo, wanda ya rasu a cikin dare.

Rasuwar Barkindo ta auku ne a ranar da ya yi wata ganawa da Shugaba Buhari, wanda ya yabe shi a matsayin wakili abin alfahari ga Najeriya.

Barkindo ya rasu yana da shekara 63 a duniya kuma shi ne Sakatare-Janar na OPEC na hudu, daga Najeriya.