✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya nada sabon Shugaban Hukumar NBC

Mista Ilelah ya maye gurbin Darakta Janar na Hukumar, Farfesa Armstrong Idachaba.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Mista Balarabe Shehu Ilelah, a matsayin sabon Darakta Janar na Hukumar NBC mai Kula da Kafafen Yada Labarai ta Kasar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya fitar ranar Juma’a a Abuja, babban birnin kasar.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Hadimin Ministan na Musamman kan Harkokin Sadarwa, Mista Segun Adeyemi, ta ce Mista Ilelah zai jagoranci Hukumar NBC na tsawon shekaru biyar a wa’adin farko.

Mista Ilelah wanda kwararren ma’aikacin jarida ne wanda ya goge a fagen watsa labaru, ya maye gurbin Mukaddashin Darakta Janar na Hukumar, Farfesa Armstrong Idachaba.

Maye gurbin Farfesa Idachaba na zuwa ne bayan kwanaki hudu da ya umarci dukkanin kafofin yada labarai na kasar da su goge tare da daina amfani da shafukansu na Twitter nan take.

Wannan umarni na zuwa ne bayan da Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ayyukan shafin Twitter a fadin kasar kan abin da ta kira yana ba da gudunmuwa wajen rura wutar rikici a kasar.