✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Buhari ya nada sabon shugaban NCPC

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Reverend Yakubu Pam a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Ziyarar Ibada ta Kirista (NCPC). Sanarwar ta ranar Asabar ta bukacin…

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Reverend Yakubu Pam a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Ziyarar Ibada ta Kirista (NCPC).

Sanarwar ta ranar Asabar ta bukacin sabon shugaban na NCPC ya kokarta wurin wanzar da aikin sabon matsayin nasa na sasanci.

Nadin na Reverend Pam ya fara aiki ne daga ranar 26 ga watan Yuni, kamar yadda sanarwar ta ce an ba shi wa’adi daya ne mai tsawon shekara biyu.

Kafin sabon nadin, Rev. Pam shi ne shugaban hukumar kula da ziyarar ibada ta Kirista da jihar Filato.