✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya nada sabon Shugaban ’Yan sandan Najeriya

Alkali Baba Usman ya zama Mukaddashin Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari, ya nada Mataimakin Shugaban ’Yan Sanda, DIG Usman Alkali Baba a matsayin sabon mukaddashin Babban Sufetan ’Yan Sandan Najeriya.

Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Maigari Dingyadi ya sanar da haka yayin ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa.

Sabon Shugaban ’Yan Sandan zai maye gurbin Mohammad Abubakar Adamu wanda shekarunsa na ritaya suka cika a farkon shekarar 2021.

A watan Fabrairun 2021, Buhari ya kara wa’adin aikin Mohammed Adamu da wata uku.

Nadin sabon Mukaddashin Babban Sufetorn ’Yan Sandan na bukatar amincewar Majalisar Shugabannin Kasa wadda zamanta ke nan tafe.