✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya nemi MTN ya rage kudin data da kira

Shugaban Kasa ya nemi MTN ya rage farashi ya kuma inganta aiki a Najeriya.

Shugaba Buhari ya bukaci kamfanin sadarwa na MTN ya rage farashin data da kira da sauran ayyukan kamfanin, lura da girman ribar da kamfanin ke samu a Najeriya.

Buhari, yayin karbar bakuncin shugabannin MTN karkashin jagorancin babban jami’inta,  Ralph Mupita a ranar Juma’a, ya bukaci kamfanin ya inganta ayyukansa a Najeriya.

“Ina taya ka murnar nada ka Shugaban kamfanin MTN. Ina kuma maka fatan alheri.

“Najeriya ce babbar kasuwar MTN a Afirka da Asiya da ma Gabas ta Tsakiya kuma ita ce kasa ta uku da kamfanin ya fi samun kudaden shiga.

“Don haka muke kiran ku kara inganta ayyukanku tare da sassauta kudaden da kuke cajin kwastomominku a Najeriya.

“A yayin da muke kokarin wadata ko’ina maganadisun sadarwar intanet cikin rahusa, muna so MTN da ya ci gaba da dafa mana wajen fadada ingantaccen layin sadarwar intanet zuwa lungu da sako na kasar nan,” inji Shugaba Buhari.

Ya kuma bukaci kamfanin na MTN da ya tallafa wa yunkurin gwamnatin na tsarin bunkasa kamfanonin sadarwa na cikin kasar.