✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya rantsar da manyan sakatarori 4 a fadarsa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, ya rantsar da wasu sabbin manyan sakatarori hudu a fadarsa ta Villa da ke birnin Abuja. Sabbin manyan…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, ya rantsar da wasu sabbin manyan sakatarori hudu a fadarsa ta Villa da ke birnin Abuja.

Sabbin manyan sakatarorin sun karbi rantsuwa gabanin a fara gudanar da zaman Majalisar Zantarwa wanda Shugaban Kasar ya saba jagoranta duk mako.

Sabbin manyan sakatarorin sun kunshi mace daya da kuma maza uku da suka zama cikon mutane 16 da aka nada a watan Yunin da ya gabata yayin da tuni aka rantsar da mutum 12 fiye da wata guda da ya gabata.

Manyan sakatarorin su ne James Sule daga jihar Kaduna da Isma’ila Abubakar daga Kebbi da Mrs Ibene Patricia Roberts daga Ribas sai kuma Shehu Aliyu Shinkafi daga jihar Zamfara.