✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya roki sarakuna su taimaka masa

Shugaba Buhari ya roki sarakuna su taimaka wa gwamantinsa wajen magance matsalolin da ke ci wa matasan Najeriya tuwo a kwarya. A zaman sirrin da…

Shugaba Buhari ya roki sarakuna su taimaka wa gwamantinsa wajen magance matsalolin da ke ci wa matasan Najeriya tuwo a kwarya.

A zaman sirrin da suka yi da shi a fadarsa da ke Abuja, Buhari ya yaba rawar da sarakunan karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ke takawa wajen kwantar da kurar da ta tashi a tarzomar zanga-zangar #EndSARS da kuma wanzar da zaman lafiya a fadin Najeriya.

“Kusancinku da jama’a ya ba ku wata dama ta musamman na iya isar da sako da kuma tababtar da ganin mun yi abin da zai yi tasiri”, inji Buhari a sanarwar da kakakinsa, Femi Adesina ya fitar bayan ganawar.

Ya shaida wa sarakunan cewa gwamantinsa ta saurari koken matasan Najeriya kuma ta tashi domin share musu hawaye, amma haka ba za ta cimma ruwa ba sai sarakuna sun shiga ciki.

“Dole sai mun shawo kan matsalar rashin tsaro, rashin aikin matasa, bunkasa masana’antu da kuma tattalin arziki na zamani”, inji shi.

Ya bayyana sarakuna a “iyayen al’umma masu kare kyawawan dabi’u”, ya kuma roke su da su yi wa kowane bangare adalci a matsayinsu na iyaye.

Sarakuna sun mika masa shawarwarin yadda zai shawo kan matsalolin da bullar annobar #coronavirus ta haddasa a kasar, kuma ya yi alkawarin zai duba da idanun basira.

Buhari ya ce matsalolin Najeriya na da girma da kuma yawan gaske ta yadda sun fi karfin a kawar da kai daga gare su ba tare da an tunkare su domin magancewa ba.

Don haka ya ce Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati, Ibrahim Gambari zai jagoranci tawagar gwamanti daga sassan Najeriya su rika ganawa kai tsaye da sarakuna domin ganin an cimma nasara a abin da aka sanya a gaba.