✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya sa a hukunta masu boye kayan abinci

Duk da yawan abincin da ake nomawa a Najeriya, farashi na tashin gwauron zabo.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya da umarnin daukar mataki a kan ’yan kasuwar da ke saye kayan abinci suna boyewa domin samun kazamar riba.

A jawabinsa ga ’yan Najeriya a ranar bikin cikar kasar shekara 61 da samun ’yanci, Buhari ya koka game da tashin gwauron zabon kayan abinci a Najeriya, duk da cewa abincin da ake nomawa a kasar ya karu sosai.

“Abin takaici shi ne duk da cewa adadin abincin da ake nomawa a kasar ya karu, farashin kayan abinci sai tashin gwauron zabo suke ta yi, saboda  miyagun ’yan kasuwa da ke sayewa suna boyewa.

“Domin magance wannan matsalar na umarci Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta Tarayya da ta farfado tare da inganta ayyukan Hukumar Kula da Adana Amfanin Gona ta Kasa;

“Sannan ta yi aiki tare da hukumomin tsaro da Hukumar Kula da Kayan Masarufi da kuma Majalisar Tarayya, domin kawo karshen wannan mummunar dabi’a da ke illata rayuwar jama’ar Najeriya,” inji Shugaba Buhari.

A cewarsa, a kokarin gwamnati na bunkasa samar da ruwan sha mai tsafta da wadataccen abinci a cikin gida, ana ci gaba da ayyukan gina sabbin dam-dam a fadin Najeriya, musamman domin taimaka wa harkar noman rani.

Ya ce,“Domin kara samar da wadataccen abinci a cikin gida, mun kammala ayyukan gina dam-dam masu yawa, muna kuma ci gaba da gyaran hanyoyin ruwa na cikin gida.